Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin ta bukaci Najeriya da ta ci gaba da goyon bayan ka’idar Sin daya tak ta yadda za ta sake jaddada aniyarta na sake haduwa cikin lumana.
A yayin bikin “Salon Kafofin watsa labarai kan ka’idar Sin daya tak a matsayin tushen dangantakar dake tsakanin Sin da Najeriya” da aka gudanar a Abuja shugaban sashen siyasa na ofishin jakadancin kasar Sin Zhu Songbo ya jaddada muhimmiyar rawar da Najeriya ke takawa a matsayin abokiyar huldar bisa manyan tsare-tsare wajen tabbatar da ikon mallakar kasa da yankin kasar Sin.
Zhu ya nanata cewa ka’idar Sin daya tilo ta amince da Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin a matsayin gwamnati daya tilo da ta wakilci kasar Sin ciki har da Taiwan wadda ya bayyana a matsayin ginshikin manufofin harkokin waje na kasar Sin da diflomasiyyar kasa da kasa.
Ya yabawa Najeriya bisa jajircewar da ta baiwa wannan matsayi musamman ma yadda ofishin kasuwanci na Taiwan an mayar da shi Dag Abuja zuwa Jihar Legas.
“Mun yaba da yadda Najeriya ke bin ka’idar Sin daya tak matsayi ne da aka kafa a cikin dokokin kasa da kasa da kuma goyon bayan kudurin Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 2758.
Muna fatan Najeriya za ta ci gaba da ba da goyon baya a kokarinmu na sake hadewar kasa cikin lumana,” in ji Zhu.
Ya jaddada cewa goyon bayan ka’idar Sin daya tilo ba lamari ne na ladabi na diflomasiyya kadai ba har ma yana taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a mashigin Taiwan.
Shugaban sashen nazarin harkokin siyasa da huldar na kasa a Jami’ar Abuja Farfesa. Sheriff Ibrahim ya ce babu wata kasa mai cin gashin kanta da za ta amince da kokarin dakushe yankinta yana mai cewa manufar Najeriya na rashin tsoma baki ta yi daidai da abin da kasar Sin ta yi tsammani kan batun Taiwan.
Ya ce “Ka’idar Sin daya tak ita ce tushen dangantakar dake tsakanin Sin da Najeriya mu tunta juna ga ‘yancin kai da hadin gwiwar tattalin arziki mai karfi tare da yawan cinikin da ya zarce dalar Amurka biliyan 20 da ayyukan samar da ababen more rayuwa da kasar Sin ke tallafawa a duk fadin Najeriya.”
Da yake goyon bayan wannan ra’ayi daraktan cibiyar nazarin kasar Sin Charles Onunaiju ya bayyana cewa amincewar da Najeriya ta yi wa birnin Beijing a matsayin gwamnatin shari’a ta kasar Sin ya kasance “mai tsarki ” ya kara da cewa duk wani yunkuri na kungiyoyin dake da alaka da Taiwan na yin tasiri kan manufofin Najeriya ko labaran kafofin watsa labarai na iya kawo cikas ga dangantakar diflomasiyya da ke tsakanin kasashen biyu.
Onuiju ya ce “Ofishin kasuwanci na Taiwan da ke Legas yana aiki ne a matsayin kungiyar da harkokin kasuwanci ba aikin diflomasiyya ba duk wani kaucewa fahimtar da aka yi daga wannan fahimtar na iya yin illa ga ginshikin dangantakar dake tsakanin Sin da Najeriya.”
Dokta Austin Maho ya bukaci kwararrun kafafen yada labarai na Najeriya da su kasance masu gaskiya da kuma taka-tsan-tsan yayin da suke ba da rahoto kan batutuwan da suka shafi yanayin kasa.
Ya jaddada bukatar daidaita bayanan da ba sa halasta Taiwan a matsayin kasa mai cin gashin kanta yana mai gargadin cewa nassosin da ke nuni da ‘yancin kai na Taiwan na iya karya manufofin Najeriya a kasashen waje.
“Mu a matsayinmu na masu aikin yada labarai dole ne mu goyi bayan manufofin harkokin waje na Najeriya. Wannan yana nufin amincewa da mutunta ka’idar Sin daya tak a cikin kalmomi da sauti ” in ji Dokta Maho.
Jami’an kasar Sin da malaman Najeriya a wurin taron sun jaddada cewa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu da mutunta ‘yancin kai da kuma kudurin tabbatar da zaman lafiya a shiyyar tsakanin Sin da Najeriya dole ne su ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen ciyar da kasar Sin gaba.
Aisha.Yahaya, Lagos