Sakataren harkokin kasuwanci na Amurka Howard Lutnick a ranar Lahadin da Ta gabata ya bayyana cewa tattaunawar da ake yi da kasar Sin a birnin Geneva na da nufin “daukar hankali” tsakanin manyan kasashen biyu kamar yadda ya yi hasashen kulla huldar kasuwanci da dama a cikin ‘yan watanni masu zuwa ba tare da bayyana takamaiman kasashe ba.
Sakataren Baitulmali Scott Bessent”ya bayyana a fili daya daga cikin manufofinsa shine rage girman kai. Ka sani 145% da 125% suna da gaske – wadannan nau’ikan kudin fito ne inda ba ku kasuwanci da juna. Don haka yana can don ganin ko za mu iya sake sasanta tattaunawar, “in jiLutnick.
Lutnick yana mayar da martani ne ga wata tambaya game da tsammanin gwamnatin Trump a tattaunawar. Yana magana ne kan harajin ramuwar gayya na Sin (China) 125% da kuma harajin Amurka 145% da aka sanya a matsayin wani bangare na yunkurin shugaban Amurka Donald Trump na amfani da manufofin kasuwanci don kara ruruta wutar masana’antu a Amurka.
“A cikin watanni uku masu zuwa wannan manufar za ta yi yarjejeniyar kasuwanci ” in ji Lutnick mai kama da kalaman da Trump ya yi akai-akai wajen kare harajin. Sai dai bai bayyana sunayen kasashen da Amurka za ta kulla hulda da su ba a wannan lokacin
A makon da ya gabata Trump da Firayim Ministan Burtaniya Keir Starmer sun ba da sanarwar wata yarjejeniyar kasuwanci tsakanin kasashen biyu.
A halin da ake ciki Lutnick ya yi watsi da rahotannin ma’aikatan jirgin ruwa da manyan motocin dakon kaya sun rasa ayyukansu sakamakon harajin kwastam.
“Wannan matsala ce ta Sin yanzu,” in ji Lutnick.
“Sauran duniya shine 10% (farashi). Don haka kada ku wuce gona da iri, “in ji Lutnick.
Ya ce “Farashi za su tsaya tsayin daka da zarar an yi wannan manufar.
Reuters/Aisha.Yahaya, Lagos