Take a fresh look at your lifestyle.

Aljeriya Da Pakistan Sun Tattauna Akan Ci Gaban Yankin.

39

Ministan harkokin wajen kasar Aljeriya Ahmed Attaf ya tattauna ta wayar tarho da mataimakin firaministan kasar Pakistan kuma ministan harkokin wajen kasar Ishaq Dar a jiya Lahadi inda suka tattauna Kan batutuwan da suka faru a yankin bayan yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin Indiya da Pakistan.

A cewar wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Aljeriya ta fitar Dar ya yi wa Attaf bayani kan yadda al’amuran yankin ke ci gaba da gudana musamman ci gaban da ya kai ga cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta.

Sanarwar ta kara da cewa “Attaf ya yi maraba da yarjejeniyar ya kuma bayyana fatansa cewa za a karfafa ta a cikin kwanaki masu zuwa don samar da zaman lafiya da adalci da kuma cikakken zaman lafiya tsakanin kasashen dake makwabtaka da juna wanda hakan zai amfanar da al’ummar kasashen biyu da kuma karfafa tsaron yankin.”

A Wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Pakistan ta wallafa a dandalin sada zumunta na yanar gizo ya ce bangarorin biyu sun amince da ci gaba da yin hadin gwiwa a dandalin tattaunawa na bangarori daban-daban don cimma matsaya guda.

Pakistan da Indiya sun sanar a ranar Asabar din da ta gabata wajen tsagaita bude wuta cikin gaggawa biyo bayan hare-haren da sojoji suka kwashe kwanaki a na kai wa juna.

Aisha.Yahaya, Lagos

Comments are closed.