Dakarun tsaron farar hula na kasar Sudan da kamfanin samar da wutar lantarki na gwamnati sun sanar da cewa sun dakile gobarar da ta tashi a tashar man da ke Port Sudan tare da fara maido da wutar lantarki a jihar Bahar Maliya bayan hare-haren da jiragen yaki marasa matuka a farkon wannan wata.
Daraktan Rundunar Tsaron farar hula ta Sudan Osman Al-Atta ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa an kashe gobarar da ta tashi a wuraren ajiyar kayayyaki da sauran wuraren da abin ya shafa a yankin Port Sudan inda ya kara da cewa ana fuskantar kalubalen kashe gobara saboda dimbin man fetur da aka ajiye a wuraren da abin ya shafa.
“An fara dawo da wutar lantarki a biranen Jihar ta Red Sea sannu a hankali,” in ji Kamfanin Lantarki.
Kwanan nan RSF ta tsananta hare-haren jiragen sama a kan wuraren soji da muhimman wurare a cikin yankunan da SAF ke iko da shi.
A ranar 4 ga Mayu an bayar da rahoton cewa RSF ta kaddamar da hare-haren jiragen sama marasa matuka kan Port Sudan babban birnin Jihar Bahar Maliya a karon farko inda suka auna sansanin sojin sama da na fari hula.
Jiragen yaki marasa matuka sun kai hari a ma’ajiyar man fetur a birnin a ranar Litinin din da ta gabata inda suka lalata su gaba daya lamarin da ya haifar da fashe-fashe masu yawa tare da haddasa gobara da ta ci kwanaki.
A ranar Talata kamfanin samar da wutar lantarki na Sudan ya sanar da cewa jirage marasa matuka ne suka kaiwa tashar taswirar wutar lantarki ta Port Sudan hari lamarin da ya kai ga katsewar wutar.
Aisha.Yahaya, Lagos