Ministan ci gaban matasa Kwamared Ayodele Olawande ya yi kira ga kwamishinonin matasa a fadin jihohi 36 na tarayyar kasar nan da su bullo da shirye-shiryen karfafa matasa a jihohinsu.
Wannan kira ya yi dai-dai da kokarin da ma’aikatar raya matasa ta tarayya ke yi na bunkasa harkokin matasa da ci gaban kasa baki daya.
Kwamared Olawande ya yi wannan kiran ne a yayin ziyarar ban girma da kungiyar Kwamishinonin Matasa na Jiha karkashin jagorancin Shugabanta Mista Gold Adedayo wanda kuma ke rike da mukamin Kwamishinan Matasa da Ci gaban al’umma a Jihar Ekiti inda aka gudanar da taron a hedikwatar ma’aikatar da ke Abuja
Da yake jawabi yayin ziyarar Ministan ya jaddada mahimmancin tsare-tsare na asali inda ya ce:
“A matsayina na wanda ya ci gajiyar shirin a gida zan iya cewa duk wani shiri da na fara tun lokacin da na yi Ministar Matasa na samu tallafi daga kungiyoyi masu zaman kansu da hukumomin da abin ya shafa abin da kuke yi na sauya rayuwar matasa a jiharku zai zama shaida ga shugabancin ku ko da bayan kun bar mulki.”
Da yake mayar da martani Mista Adedayo ya bayyana cewa ziyarar da biyo bayan wata ganawar da Ministan ya yi da kungiyar Forum a Legas inda aka cimma matsaya kan muhimman batutuwan da suka shafi aiki.
Ya zayyana muhimman abubuwa guda uku da ke bukatar goyon bayan Ministan: Samar da Dakin Taro na Musamman: Kungiyar ta bukaci kebe wuri a cikin harabar ma’aikatar da ke Abuja don zama hedkwatarta da kuma sauƙaƙe tarurruka akai-akai.
Gudanar da Ayyukan Jihohi: Kungiyar ta yi kira ga Ministan da ya taimaka wajen samar da hanyoyin hadin gwiwa da kuma ziyartar jihohi daban-daban don ayyukan da suka shafi matasa.
Taro na yau da kullun: Dandalin na shirin fara taruka akai-akai inda za a fara da zama mai zuwa a Bayelsa.
“Wadannan su ne mahimman tubalan ginin da ake bukata don tabbatar da nasarar shirye-shiryen ci gaban matasa a duk faɗin ƙasar,” Adedayo ya tabbatar.
Babban Sakataren Ma’aikatar Mista Olubunmi Olusanya yayin da yake maraba da tawagar ya nanata kudurin ma’aikatar da tallafawa dandalin.
Ya kuma tabbatar wa da kwamishinonin cewa ma’aikatar a shirye take da goyon bayan duk wani kokari da aka yi na inganta matasan Najeriya.
Aisha.Yahaya, Lagos