Take a fresh look at your lifestyle.

Poland Ta Hana Shugaban Sabiyawan Bosnia Dodik Daga Yankinta 14/5/25

40

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Poland ta ce ta haramtawa jagoran ‘yan awaren Sabiyawan Bosnia Milorad Dodik shiga cikin kasarta kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen kasar ta bayyana a ranar Talata da ta gabata a daidai lokacin da ake fama da rikicin siyasa a yankin Balkan inda ake nemansa da laifin kai wa kundin tsarin mulkin kasar hari.

Matakin na nufin Poland ta bi sahun Jamus da Ostiriya wajen hana Dodik wanda ya janyo rikicin siyasa mafi girma a Bosnia tun bayan kawo karshen yakin kasar a shekarun 1990 bisa zargin kin bin hukumce-hukumcen da wakilin kasa da kasa ya yi wanda aikinsa shi ne hana kasar da ke da kabilu daban-daban sake komawa cikin rikici.

Ma’aikatar harkokin wajen Poland ta ce “An fara wata hanya game da hana shiga kasar Milorad Dodik” in ji ma’aikatar harkokin wajen Poland a cikin imel.
“Tsarin yana ci gaba za a kammala shi nan da ‘yan kwanaki.”

Ofishin yada labarai na jam’iyyar Dodik bai amsa ba nan take kan bukatar da aka aiko ta imel don yin tsokaci.

Wakilin zaman lafiya na kasa da kasa na Bosnia Christian Schmidt ya ce a cikin watan Afrilu ya bayar da umarnin dakatar da duk wani kasafin kudi na jam’iyyar Dodik.

Rundunar ‘yan sandan jihar Bosnia SIPA ta yi kokarin cafke Dodik a watan Afrilu amma jami’an ‘yan sandan suna dauke da makamai sun hana shi.

Reuters/Aisha.Yahaya, Lagos

Comments are closed.