Take a fresh look at your lifestyle.

Tanzaniya Ta Tsare Babban Dan Adawa

44

Gwamnatin Tanzaniya ta kama wani babban jami’in ‘yan adawa Amani Golugwa a lokacin da yake shirin tafiya Belgium don wani taron siyasa in ji jam’iyyarsa a ranar Talata da ta gabata Lamarin dai ya haifar da sabon fargaba game da yuwuwar murkushe ‘yan adawa gabanin zaben kasar na watan Oktoba.

Shugabar kasar Samia Suluhu Hassan da ke neman tazarce ta sha nanata kudurin gwamnatinta na kare hakkin dan Adam. Duk da haka kama manyan mutane na baya-bayan nan ya jawo ƙarin bincike ga tarihinta.

An kama Golugwa wani jigo a babbar jam’iyyar adawa ta CHADEMA ta Tanzania a filin jirgin sama na Julius Nyerere da ke babban birnin Dar es Salaam ranar Litinin da ta gabata jam’iyyarsa ta rubuta a kan X.

‘Yan sandan Tanzaniya sun tabbatar da kama shi a wani sakon da suka wallafa a shafinsu na Instagram inda suka rubuta cewa Golugwa “yana da dama fitowa da komawa kasar ba tare da bin ka’idojin doka ba.”

Sanarwar ta kara da cewa “Yankin musamman na ‘yan sanda na Dar es Salaam na ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin tare da hadin gwiwar wasu jami’an tsaro.”

Mai magana da yawun gwamnati bai amsa bukatar jin ta bakinsa ba.

Golugwa dai ya kamata ya wakilci jam’iyyarsa a Brussels a wani taron da kungiyar International Democracy Union ta shirya kungiyar masu ra’ayin mazan jiya da CHADEMA ta ke da kuma ke kirga ‘yan Conservative na Burtaniya da ‘yan Republican na Amurka a matsayin mambobi.

“IDU ta yi kakkausar suka ga kamawa da cin zarafin CHADEMA’s (Golugwa) ba bisa ka’ida ba” kungiyar ta buga a kan X. “Kashe muryoyin ‘yan adawa ya saba wa jigon dimokuradiyya. Muna kira da a sake shi cikin gaggawa.”

‘Yan sanda sun kama Tundu Lissu shugaban CHADEMA kuma babban Dan adawar Tanzaniya a watan jiya. Lissu wanda aka harbe har sau 16 a harin da aka kai a shekarar 2017 ya zo na biyu a zaben shugaban kasar da ta gabata daga bisani an tuhume shi da laifin cin amanar kasa kan abin da masu gabatar da kara suka ce jawabi ne da ke kira ga jama’a da su yi tawaye tare da kawo cikas ga zaben.

Ya gudanar da tarurruka da dama a farkon watan Afrilu mai taken “Babu Sauyi Babu Zabe” inda kungiyar CHADEMA ta bukaci sauye-sauye a tsarin zaben da suka ce yana goyon bayan jam’iyya mai mulki.

Reuters./Aisha.Yahaya, Lagos

Comments are closed.