Take a fresh look at your lifestyle.

Dangote Ya Gaisa Da Shugaba Trump A Qatar

51

Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka Aliko Dangote na cikin wadanda suka yi musabaha da shugaban kasar Amurka Donald Trump, a ziyarar da ya kai Qatar a jiya.

Wani faifan bidiyo da ake yadawa ya nuna yadda aka gabatar da Dangote ga shugaban kasar Amurka yayin ziyarar da Sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani ya kai masa.

Tun da farko Sarkin ya yi maraba da Trump da kansa a lokacin da ya isa filin jirgin saman Hamad wanda ke zama farkon zango na biyu na ziyarar Trump a Gabas ta Tsakiya.

liyafar ta hada da wani jirgin saman yaki na Air Force One da kuma ayarin motocin da ke dauke da Tesla Cybertrucks. Bayan isowarsa Trump da Al Thani sun halarci bikin sanya hannu kan wata muhimmiyar yarjejeniya tsakanin Qatar Airways da Boeing. Yarjejeniyar ta shafi siyan jiragen Boeing har guda 210 wanda darajarsu ta kai kusan dalar Amurka biliyan 96 wand hakan ya zama mafi girma a tarihin Boeing.

Ziyarar ta kuma jawo hankulan jama’a saboda tayin Qatar na wani katafaren jirgi kirar Boeing 747-8 wanda aka kiyasta dala miliyan 400 wanda aka yi niyya a matsayin wanda zai maye gurbin Air Force One. Wannan karimcin ya haifar da mahawara tsakanin bangarorin biyu a Amurka dangane da da’a da halaccin karbar irin wannan kyauta daga gwamnatocin kasashen waje.

A cikin faifan bidiyon an ga Dangote suna gaisawa da shugaban Amurka kafin kuma (Dangote) ya zarce domin mika gaisawa ga Sarkin.

Babu tabbas kan takamaiman batutuwan da aka tattauna tsakanin hamshakin attajirin da shugaban Amurka.

Trump ya samu rakiyar wata tawaga na wasu fitattun ‘yan kasuwan Amurka da suka hada da Elon Musk

Aisha.Yahaya, Lagos

Comments are closed.