Take a fresh look at your lifestyle.

An Yi Garkuwa Da Jagoran Dan Adawa Congo A Brazzaville

53

Wasu mutane dauke da makamai da fuskansu a rufe inda su ka yi garkuwa da shugaban jam’iyyar adawa ta Les Socialist Kongo Dan takara Lassy Mbouity a zaben shugaban kasar Kongo a watan Maris na 2025 a Brazzaville kwanaki kadan bayan tsira daga yunkurin kisan gilla.

Jam’iyyarsa ta zargi gwamnati.
“Mun gamsu da mulkin kama-karya na Brazzaville a baya. Wannan ba shine karo na farko ba. An kama shi kwanakin baya kuma mutanen da suka zo gidansa da fuskansu a rufe dauke da makamai da kuma amfani da mota marar lamba. Martial Mbourangon Pa’nucci kakakin jam’iyyar Les Socialistes Congolais ya bayyana haka.

Jam’iyyun adawa da dama sun bi sahun jam’iyyar Les Socialistes Congolais don fitar da wata sanarwa da hadin gwiwa a ranar Alhamis da ta gabata inda suka yi Allah wadai da sace shi tare da neman a sako Mbouity ba tare da wani sharadi ba.

“Wannan aiki na matsorata wani bangare ne na tashin hankali na ta’addanci da tsoratarwa da kuma take hakkin bil’adama na tsare-tsare a jamhuriyar Kongo. Wannan babban cin zarafi ne na ‘yancin kai da kuma keta doka ta 9 na kundin tsarin mulkin 25 ga Oktoba 2015. Muna bukatar a gaggauta sakin Lassy Mbouity.” Clément Mierassa shugaban jam’iyyar Social Democratic Party ta Congo ya ce.

Kungiyar Kare Hakkokin Dan Adam ta Kongo ita ma ta shiga cikin jerin gwano inda ta yi kira da gaggawa na neman taimako daga jami’an diflomasiyya da hukumomin kasa da kasa.

Har yanzu gwamnati ba ta mayar da martani kan zargin yin garkuwa da mutane ba.

Africanews/Aisha

Comments are closed.