Shugaban Hukumar kula da ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje (NiDCOM) Dr. Abike Dabiri-Erewa ta taya Dr. Adekunle Osibogun Princess Opeyemi Bright Cllr da Jason Utitofon Jackson da Sunny Lambe akan nasarar da suka samu a zaben da aka gabatar.
A cikin wani sakon taya murna da Mista Gabriel Odu na sashin hulda da jama’a da kuma ladabi na hukumar ya fitar Dabiri Erewa ta yabawa mutanen biyu na Cllr. Opeyemi Bright da Cllr. Jason Utitofon Jackson saboda karya tarihin magajin gari da Kuma Bakar fata na farko . Ta kuma taya Sunny Lambe kansila da Adekunle Osibogun domin sake zabensu a matsayin Kansiloli.
Shugaban NIDCOM ta bayyana nasarar a matsayin wani tarihi ne wanda ke nuna kwazo dajajircewa da kokarinsu na samun nasara.
Dabiri-Erewa ta bukace su da su ci gaba da jajircewa wajen gudanar da ayyukansu. Ta kuma roki Allah ya ba su kariya da karfi da kuma shugabanci a sabbin mukamansu tare da kara musu kwarin gwiwa da su ci gaba da yin iya kokarinsu wajen gudanar da ayyukansu.
Yayin da aka sake zaben Dokta Adekunle Osibogun a matsayin Kansila ga Majalisar Buckinghamshire da Buckingham Town Council da. Gimbiya Opeyemi Bright ta kafa tarihi a matsayin magajin gari mafi karancin shekaru a gundumar Barking & Dagenham na London.
Cllr. Jason Jackson sabon Magajin Garin Islington ta wannan matakin shine bakar fata na farko da aka zaba a wannan matsayi da kuma Cllr. Sunny Lambe wanda ya yi hidimar Karamar Hukumar tare da bambanci shekaru da yawa yanzu ya karbi mukamin sabon Magajin Garin Southwark.
A wani labarin kuma Shugaban Hukumar NiDCOM Dr. Abike Dabiri-Erewa ta taimaka wajen dawo da Adeola diyar jaruma Jumoke George daga kasar Mali.
Inda an tuna cewa Adeola ‘yar shekara 41 fitacciyar jarumar yarbawa Jumoke Georgeb an same ta ne a kasar Mali bayan an bayyana bacewar ta tsawon shekaru hudu.
A baya Jumoke (mahaifiyar) ta bayyana bacewar a yayin wata hira da aka yi da ita a shirin Talk to B wanda jaruma Abiola Bayo ta shirya.
Ta bayyana cewa Adeola ta kasance tare da kakarta a Ibadan kuma an ganta a karshe bayan ta sanar da iyaye ta ji ta Legas.
Aisha.Yahaya, Lagos