Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaban Kasa Tinubu Ya Dawo Abuja Daga Rome

37

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dawo Abuja daga birnin Rome bayan ya halarci bikin rantsar da Paparoma Leo na 14.

Jirgin shugaban da ke jigilar shugaban ya sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe Abuja da karfe 07:00 na yammacin ranar Talata.

Ministan babban birnin tarayya Nyesom Wike da sakataren gwamnatin tarayya George Akume da shugaban jam’iyyar All Progressives Congress Party Dr. Abdullahi Ganduje da sauran manyan jami’an gwamnati sun tarbi shugaba Tinubu.

Shugaban ya tashi daga Abuja zuwa birnin Rome a ranar Asabar 17 ga watan Mayu domin halartar taron kaddamar da sabon shugaban cocin Roman Katolika na Fafaroma Leo na 14.

Shugaban Najeriya ya kai ziyarar ne bisa gayyatar da fadar Vatican ta yi masa biyo bayan zaben da Kwalejin Cardinal ta yi wa Fafaroma Leo na 14 a kwanan baya inda ta dora shi Pontiff na 267 kuma Bishop na Rome.

A yayin da ya isa birnin Rome a ranar Asabar din da ta gabata babban sakataren harkokin wajen fadar Vatican Cardinal Pietro Parolin ya shirya liyafar cin abincin dare inda ya jaddada aniyar Najeriya na inganta tattaunawa da juna da hakuri da juna a fadin duniya.

A wajen taron shugaba Tinubu ya nanata budewar Nijeriya ga abokantaka da dangantakar addinai da jajircewa wajen gina fahimtar juna a fadin duniya.

A ranar Lahadi  din  da ta gabata ne shugaba Tinubu ya hadu da shuwagabannin duniya a St Peter’s Basilica domin bukin rantsar da Paparoma Leo na 14 wanda tsohon Cardinal Robert Francis Prevost haifaffen Chicago ne Augustinian.

Shugaban na Najeriya ya yabawa lso ya yi musabiha mai dadi da Mai Martaba Paparoma Leo na 14 a fadar Vatican bayan kammala taron majalissar da aka fara na sabon Fafaroma.

Haɗin gwiwar da shugaban ya yi tare da Paparoma Leo XIV ya ƙara yawan jerin ayyukan kasa da kasa da aka yi niyya don samar da zaman lafiya  haɗin kai da hadin gwiwa a tsakanin addinai da al’adu.

 

 

Aisha.Yahaya, Lagos

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Comments are closed.