Majalisar Wakilai ta bukaci Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) da ta samar da kayan agaji da sauran taimakon da suka dace ga al’ummomin da abin ya shafa sakamakon mummunar iska da ruwan sama da suka addabi wadannan al’umma.
Majalisar ta bukaci Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta yi gaggawar gudanar da tantance bala’i a yankunan da abin ya shafa; Al’ummar Jeddo Ugbokodo da Ughoton a karamar hukumar Okpe ta Jihar Delta.
Kudurin ya biyo bayan amincewa da kudirin “Mahimmancin Gaggawa ga Jama’a kan bukatar gaggawa ta Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) a garuruwan Jeddo da Ugbokodo da Ughoton da ke karamar hukumar Okpe ta Jihar Delta kan mummunar iska da ruwan sama da ta addabi al’ummar Jihar,”Mista Etanabene ya gabatar.
Da yake jagorantar muhawarar kan kudirin Mista Etanabene ya ce majalisar ta lura da mummunar iska da ruwan sama da ta addabi al’ummomin Jeddo da Ugbokodo da Ughoton na karamar hukumar Okpe ta Jihar Delta a ranar 15 ga Afrilu 2025.
“Har ila yau lura da cewa barnar da guguwar ta yi wa al’ummar Jeddo da Ugbokodo da Ughoton ba a taba yin irinsa ba wanda ya yi barna da dukiyoyi da sauran hanyoyin rayuwa na al’ummar yankunan da abin ya shafa wanda ya kai daruruwan Miliyoyin Naira.
“Sanin cewa rufin gidaje sama da dubu biyu ya lalace gaba daya da daruruwan gine-gine da muhimman ababen more rayuwa kamar wutar lantarki da na’urorin sadarwa ba su tsira ba kuma dubban mazauna wadannan al’ummomin sun zama marasa gida.
“Abin mamaki cewa al’ummamomin mazauna garin da abin ya shafa na matukar bukatar agaji don dakile illar bala’in da ya same su.” Kudirin ya ce.
A cewar dan majalisar ya yi imanin cewa idan ba a dauki matakan gaggawa ba na kai dauki ga al’ummar da abin ya shafa domin kuwa abin da suke rayuwa ya kare tare da wannan mawuyacin lokaci na tasirin tattalin arzikin kasa hakan zai haifar da matsala ga jama’a.
an yi kira da a samar da matsuguni na gaggawa kayan gini da Kayan da taimakon kudi da kula da lafiya na bukata ga wadanda abin ya shafa.
Da yake yanke hukunci kan kudirin kakakin majalisar Mista Tajudeen Abbas ya yi tsokaci tare da umurtar kwamitin majalisar kan bada agajin gaggawa da bala’o’i da ya tabbatar da bin doka da oda.
Aisha. Yahaya, Lagos