Mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ya isa Jalingo babban birnin Jihar Taraba a wata ziyarar aiki a jihar.
Mataimakin shugaban kasa ya sauka a filin jirgin saman Danbaba Suntai dake Jalingo da misalin karfe 9:17 agogon GMT
VP Shettima ya samu tarbi daga gwamnan Jihar Kefas Agbu da mambobin majalisar zartarwa ta Jihar Taraba
Jim kadan bayan isowar mataimakin shugaban kasar ya karzaya inda zai kaddamar da filin jirgin saman Danbaba Suntai da aka gyara a Jihar.
Daga nan ne ya ci gaba da kaddamar da sabon dakin liyafa da aka gina a harabar gidan gwamnati Jalingo.
Haka kuma zai bude wani dandalin zuba jari na kasa da kasa a Taraba karon na farko 2025.
Aisha.Yahaya, Lagos