Pakistan ta sanar a ranar Laraba din Dan ta gabata cewa ta amince da hadin gwiwar cinikayya da zuba jari tare da kasar Sin kwanaki kadan bayan kawo karshen kazamin fadan sojan da ta yi da Indiya cikin kusan shekaru 30 rikicin da Beijing ta bukaci bangarorin biyu su warware cikin lumana.
Tsagaita bude wuta da aka ayyana a ranar 10 ga watan Mayu ya biyo bayan kazamin fadan da aka kwashe kwanaki hudu ana gwabzawa tsakanin makwaftan biyu masu dauke da makamin nukiliya. Tashin hankali ya barke bayan wani mummunan harin da aka kai ranar 22 ga watan Afrilu a yankin Kashmir da ke karkashin ikon Indiya ya kashe mutane 26. Indiya ta zargi Pakistan da kai harin zargin da Islamabad ta musanta.
Ministan harkokin wajen Pakistan Ishaq Dar ya gana da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi a ranar Talata din da ta gabata a birnin Beijing inda suka tattauna batutuwan da suka shafi kasashen biyu da na shiyya-shiyya.
A cewar ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang ya jaddada goyon bayanta ga ‘yancin kai da ‘yancin fadin kasar Pakistan kana ya karfafa gwiwar kasashen Pakistan da Indiya da su magance sabanin dake tsakaninsu ta hanyar tattaunawa.
Ma’aikatar harkokin wajen Pakistan ta ce bangarorin biyu sun amince da karfafa hadin gwiwa da dama da suka hada da ciniki da zuba jari da noma da raya masana’antu. A waje guda kuma Dar da Wang sun yi wata ganawa da mukaddashin ministan harkokin wajen Afghanistan Amir Khan Muttaqi. Mutanen uku sun amince da fadada hanyar tattalin arziki tsakanin Sin da Pakistan (CPEC) zuwa Afganistan da zurfafa hadin gwiwa a karkashin shirin Sin na Belt da Road Initiative. Za a gudanar da taron koli na uku a gaba a birnin Kabul kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen Pakistan ta tabbatar.
Reuters/Aisha. Yahaya, Lagos