Yayin da Najeriya Ke bi sahun duniya wajen bikin ranar bambancin al’adu da tattaunawa don ci gaba a bana uwargidan shugaban kasa Oluremi Tinubu ta bukaci ‘yan Najeriya da su hada kai wajen ciyar da kasar gaba.
A cikin sakonta na tunawa da ranar Mrs Tinubu ta ce ya kamata bambance-bambancen da ke tsakanin al’ummar kasar su kara karfafa dankon zumuncin da ke tsakanin ‘yan Najeriya.
Ta ce: “Rana ta Duniya don bambancin al’adu don tattaunawa da ci gaba da nuna babban ƙarfin da ke tattare da bambance-bambancen da ke tsakaninmu da kuma bil’adama daya wanda ya haɗu mu duka.Hakika akwai karfi da haɗin kai a cikin bambancin.
“Alal misali Najeriya tana da kabilu sama da 250 kowannensu yana magana da yare daban amma ta hanyar tattaunawa da mu’amalarmu da mutunta juna ne muke samun hakikanin gaskiya da hadin kai.”
Uwargidan shugaban kasar ta bukaci ‘yan kasar da su ci gaba da gudanar da bukukuwan al’adun gargajiyar Nijeriya da kuma kiyaye su.
“A wannan rana ina karfafa wa kowane dan Najeriya kwarin gwiwa da ya yi bikin albarkar al’adunmu mu saurare shi cikin tausayawa mu yi jagoranci cikin fahimta mu rungumi wannan tafiya tare da samar da kyakkyawar makoma ga Nijeriya da ma duniya baki daya.
“Ranar Duniya mai farin ciki don bambancin al’adu don tattaunawa da ci gaba,” in ji Misis Tinubu.
Aisha.Yahaya, Lagos