Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaba Tinubu Ya Taya Fitaccen Dan Siyasa Sanata Abe Cika Shekaru 60 A Duniya

303

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya taya fitaccen dan siyasa lauya kuma tsohon Sanata mai wakiltar Ribas ta kudu maso gabas Sanata Magnus Ngei Abe murnar cika shekaru 60 a duniya.

Shugaba Tinubu ya bayyana irin gudunmawar da Sanata Abe yake bayarwa ga kasar nan da kuma jajircewarsa na samar da zaman lafiya da hadin kai ba a jihar Ribas kadai ba har ma a yankin Neja Delta baki daya.

Shugaban ya kuma lura da gagarumin aikin Sanata Abe a matsayin Kwamishinan Yada Labarai da Sakataren Gwamnati a Jihar Ribas daga 2003 zuwa 2007.

Shugaba Tinubu a wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawunsa Mista Bayo Onanuga ya bayyana Sanata Abe a matsayin abokin siyasa wanda ya ci gaba da yin hadin gwiwa da shi a cikin muradinsa na samar da karfi mai karfin da tattalin arziki da kuma hada kan Najeriya karkashin shirinsa na Renewed Hope.

A yayin da Sanata Abe ke bikin cika shekaru 60 a duniya shugaba Tinubu ya mika masa fatan alheri tare da yi masa addu’ar karin shekaru masu yawa na tasiri da nasara ga Sanatan.

Sanata Magnus Abe ya lashe zabensa na farko a Majalisar Dattawa a watan Afrilun 2011 an sake zaben 2016 ya sake samun wani wa’adi.

 

Aisha.Yahaya, Lagos

Comments are closed.