Hukumar alhazai ta kasa NAHCON, ta sabunta lasisin gudanar da aikin Hajji na hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kwara domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2026.
Sanarwar ta fito ne daga bakin ko’odinetan shiyyar NAHCON a Jihohin Kwara, Ondo, da Ekiti da Alhaji Lawal Kaseem Yinka, a wata ziyarar ban girma da ya kai hedikwatar hukumar da ke Ilorin babban birnin Jihar Kwara.
Alhaji Yinka ya bayyana cewa “an sabunta ne bayan wani nazari mai zurfi ya tabbatar da cewa hukumar ta cika dukkan ka’idojin gudanar da aiki da kuma yanayin shirinta.”
“Mun gamsu sosai da kayan aiki, da tsarin gudanarwa da Hukumar Jihar Kwara ke aiwatarwa,” in ji Alhaji Yinka.
Yace; “Wannan sabuntawar haske ne ga duk mahajjata daga Jihar Kwara, ciki har da wadanda ba ‘yan asalin kasar nan ba, don fara shirye-shiryensu na tafiya ta ruhaniya na 2026.”
Babban Sakataren Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kwara, Alhaji Abdulsalam Abdulkadir ne ya karbi bakuncin tawagar NAHCON.
Ya samu wakilcin babban jami’in gudanarwar, Hajia Ramat Alaaya, tare da wasu manyan jami’an gudanarwa.
Bayan kammala taron, tawagar ta duba wasu muhimman sassa da suka hada da sashen sarrafa bayanai, sashen asusu, dakin taro, ofisoshin gudanarwa, sashin sayayya, sashin yada labarai, da kuma sashin tsare-tsare, inda ya kara nuna kwazon gudanar da hukumar
Aisha.Yahaya, Lagos