Take a fresh look at your lifestyle.

Najeriya Tayi Allah-wadai Da Karuwar Kashe-kashe Da Sace-sacen jama’a A Afirka Ta Kudu

22

Gwamnatin Najeriya ta bayyana damuwarta kan karuwar kashe-kashe da sace-sacen ‘yan kasarta da ke zaune a wasu biranen kasar Afirka ta Kudu.

Karamin Ministar Harkokin Wajen Kasar, Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu, ta bayyana hakan ne a yayin da ake rattaba hannu kan wata yarjejeniya kan harkokin siyasa da Mataimakin Ministan Hulda Da Kasa da Kasa na Afirka ta Kudu, Thandi Moraka, a Abuja.

Ambasada Odumegwu-Ojukwu ta ce ‘yan Najeriya sun damu matuka game da yadda ake samun karuwar kashe-kashen ba bisa ka’ida ba, da kuma yadda ake samun tsaikon shari’ar da ake yi a kotu kan wadanda ake zargi da kisan kai, wadanda da yawa daga cikinsu, a cewarta, galibi suna bacewa ba tare da gano su ba bayan an bayar da belinsu.

Ta kuma bayyana kalubalen da ma’aikatun Najeriya a Pretoria da Johannesburg ke fuskanta wajen samun rahotannin binciken gawarwaki da bayanai daga ‘yan sandan Afirka ta Kudu kan shari’o’in da suka shafi ‘yan Najeriya da suka mutu ko suka bace.

Ministan ya ce; “Mun samu rahotanni da dama kan matsalolin da al’ummar Najeriya ke fuskanta wajen samun bayanai kan inda ‘yan kasar da aka sace suke, da kuma jinkirin shari’ar da ake yi a kotu da ke da alaka da cin zarafin ‘yan Najeriya.”

Ministan, ya bayyana fatansa cewa, rattaba hannu a kan tsarin yin gargadin farko zai karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, da kuma samar da mafita mai dorewa kan matsalolin da aka taso.

Ambasada Odumegwu-Ojukwu ya jaddada aniyar Najeriya na fadadawa da kuma karfafa dabarun hadin gwiwa da kasar Afirka ta Kudu.

A nata martanin, mataimakiyar ministar huldar kasa da kasa da hadin gwiwar kasa da kasa ta Afirka ta Kudu, Thandi Moraka, ta yi alkawarin cewa gwamnatinta na yin iyakacin kokarinta wajen kare dukkan ‘yan kasashen waje da ke zaune a kasar.

Ina so in tabbatar wa al’ummar Najeriya cewa matsayin da wata kungiya mai suna Dudula-Dudula ta dauka baya wakiltar manufofin gwamnatin Afirka ta Kudu,” in ji Ms Moraka.

Madam Moraka ta ci gaba da cewa, batutuwan da aka tabo suna daukar hankali a karkashin jagorancin shugaba Cyril Ramaphosa, inda ta kara da cewa ana kara zage damtse wajen kare ‘yan kasashen waje da ke zaune bisa doka a Afirka ta Kudu.

Ta sake nanata cewa Afirka ta Kudu ta kasance kasa mai maraba, ta kuma bukaci dukkan bakin haure da su shiga kasar ta hanyoyin da suka dace.

 

Comments are closed.