Shugaban kasar Namibiya Netumbo Nandi-Ndaitwah ya sauke Natangwe Ithete daga mukaminsa na mataimakin firaminista kuma ministan masana’antu, ma’adinai da makamashi, fadar shugaban kasar ta bayyana a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi.
“Don tabbatar da ci gaba da ingantaccen aiki a cikin wannan muhimmin bangare, Shugaba Nandi-Ndaitwah zai dauki nauyin Ma’aikatar Masana’antu, Ma’adinai da Makamashi, nan da nan,” in ji sanarwar.
Bai Bada Dalili Ba.
An nada Itthete kan mukaman a watan Maris a matsayin wani bangare na sabuwar gwamnatin Nandi-Ndaitwah. Ya ci gaba da zama Dan majalisa, in ji sanarwar.
Namibiya na shirin hako danyen mai na farko a shekarar 2030 bayan wasu manyan bincike da aka yi a shekarun baya-bayan nan. Yana hako kayayyaki kamar uranium da lu’u-lu’u.
Reuters/Aisha.Yahaya, Lagos