Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rantsar da Justice Olukayode Ariwoola a matsayin babban alkalin alkalan Najeriya.
An rantsar da mai shari’a Ariwoola ne a ranar Laraba a zauren majalisar kafin a fara taron majalisar zartarwa ta tarayya.
Bikin ya samu halartar mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Ibrahim Gambari, shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya Dr Folashade Yemi-Esan.
Sauran sun hada da alkalan kotun koli, gwamnonin jihohin Oyo da Ondo, Sheyi Makinde da Rotimi Akeredolu.
An nada Mai Shari’a Ariwoola a matsayin Alkalin Alkalan Najeriya (CJN) ne a ranar 27 ga watan Yunin wannan shekara, bayan murabus din da magabacinsa, Mai shari’a Tanko Muhammad ya yi bisa dalilan lafiya. Sabon CJN ya kasance yana yin aiki tun daga lokacin.
A tattaunawarsa ta farko da manema labarai jim kadan bayan rantsar da shi, CJN ya yi kira ga ‘yan siyasa da su bar shari’a ta rinka aiki yadda ya kamata ganin yadda zaben 2023 ke gabatowa yayin da ya yi alkawarin kawo sauyi a kotun kolin kasar.
Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo, wanda shi ma ya zanta da ‘yan jarida, ya bayyana godiyar shi ga shugaba Buhari a madadin Al’umar jihar sakamakon nada daya daga cikinsu a matsayin Alkalin Alkalan Najeriya
A halin da ake ciki, Shugaba Buhari yana jagorantar wani taro na zahiri na Majalisar Zartarwa ta Tarayya tare da wasu Ministoci daga ofisoshi daban-daban a Abuja.
Kafin a fara taron, majalisar ta yi shiru na minti daya domin karrama tsohon ministan ayyuka na musamman, Vincent Ogbulafor, wanda ya rike mukamin minista a gwamnatin Olusegun Obasanjo.
Leave a Reply