Take a fresh look at your lifestyle.

KUNGIYAR MATASAN AREWA TA KARRAMA DARAKTAN KULA DA SASHEN NAURAR ZAMANI (VON)

2 345

Kungiyar matasan Arewa ta Najeriya,ta bada lambar yabo ga daraktar kula da sashen anfani da naurar zamani mai yatsu (DIGITAL MEDIA) Hajia Hadiza Sani.

 

An gudanar da bukin mika lambar yabon ne a shelkwatar muryar Najeriya (VON) dake babban birnin tarayya Abuja.

 

Kafin mika lambar yabon,sakataren hulda da jama’a na kungiyar, Mallam Abdullahi Bilal yayi bayanin dalilin suka ga Hajia Sani ta cancanta a baTa lambar yabo.

Abdullahi yace: “Muna bada lambar yabo ne ga ‘yan Arewa da suka taka rawar gani a fanonin daban – daban a Najeriya,kuma Hajia Sani na daya daga cikin ‘yan arewa da suka bada gudmmowa a bangaren yada labarai ta hanyar anfani da naurar zamani mai yatsu wato digital’’.

 

Mallam Abdullahi ya bada misali da irin ci gaba da magabatan Najeriya suka kawo ma kasar irin su, Sir.Ahmadu Bello Sardauna da Abubakar Tafawa Balewa.

A nata jawabin godiya, Daraktan sashen anfani da Naurar zamani a yanar  Gizo, Hajia Sani,ta yaba da wannan karamcin da kungiyar ta nuna mata.

 

Da farko nagode wa Allah da ya bani tsawon rai da basira,ya kuma kawo ni wannan lokaci da wata kungiyar Arewa ta yaba da aikin da nake gudanarwa,ta karrama ni da babbar lambar yabo domin irin rawar da nake takawa a bangaren yada labaran abubuwan ci gaban Najeriya ta yanar gizo a nan Muryar Najeriya da ma wasu aiyyukan ci gaban da nake gudanarwa domin hada kan al’umma da wanzar da zaman lafiya. Ina kira ga ‘yan Najeriya,Dole ne mu tashi tsaye mu hada kai domin samar da zaman lafiya ta yadda sauran kasashen duniya zasuyi koyi da mu a matsayin mu na babbar kasa a Nahiyar Afirka”.

 

Mallam Abdullahi yayi bayanin irin gudummowar da kungiyar su ke samarwa a yankunan Arewacin Najeriya inda suke zagayawa sako- sako domin shirya taron bita na wayar da kan Matasa game da zama masu kishin kasar su,da horas das u sanao’in dogaro da kai,da kuma kaucewa shiga bangar siyasa.

2 responses to “KUNGIYAR MATASAN AREWA TA KARRAMA DARAKTAN KULA DA SASHEN NAURAR ZAMANI (VON)”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *