Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen Jihar Ebonyi, dake kudu maso gabashin Najeriya, ta karbi sabbin mambobinta da suka sauya sheka daga jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP).
Shugaban jam’iyyar APC na zJihar, Mista Stanley Okoroemegha, ne ya bayyana hakan jim kadan bayan karbar sabbin mambobin a ofishinsa da ke Abakaliki, babban birnin Jihar.
Emegha ya ce makasudin hada kowa da kowa shi ne don tabbatar da cewa wadanda suka yi wa Jihar hidima kuma har yanzu suna son bayar da gudummawar kason su an hada su don tallafa wa gwamnati mai ci ta yadda za ta cimma burinta, wato Kundin Bukatun Jama’a.
“Ya zuwa ranar 28 ga wannan wata, Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Ohaozara/Onicha/Ivo, Mista Nkemkama Kama, zai koma jam’iyyar, ko a watan Disamba ma wasu irin su Idu Igariwey, mai wakiltar mazabar tarayya ta Afikpo/Edda, za su shiga, muna iyakar kokarinmu wajen hada kan masu ruwa da tsaki a Jihar,” inji shi.
Shugaban na Jihar ya kara da cewa sauya shekar da ake yi ta samo asali ne sakamakon tasirin Gwamna Nwifuru ga al’ummar Jihar.
Sabbin mambobin kungiyar karkashin jagorancin tsohon kwamishinan kudi na Jihar Barista Timothy Odah, sun isa sakatariyar jam’iyyar APC ta Jihar Abakaliki tare da dimbin magoya bayanta, wadanda suka rera wakokin hadin kai ga jam’iyyar.
Aisha. Yahaya, Lagos