Lamido Yayi Kira Da A Rusa Babban Taron Zaben PDP Na Badun
Tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya bayar da wa’adin kwanaki 10 ga jam’iyyar PDP da ta warware rikicin cikin gida inda ya bukaci da a rusa taron zaben Ibadan da aka yi kwanan nan tare da gaggauta kafa kwamitin riko na kasa.
Lamido ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake jawabi ga daruruwan magoya bayansa da suka hada da tsaffin shugabannin kananan hukumomi tsofaffin kwamishinoni da sauran masu rike da mukaman siyasa wadanda suka kai masa ziyarar hadin kai a ofishinsa na Sharada da ke Kano.
Ya nuna matukar damuwarsa kan rikicin da ke faruwa a cikin jam’iyyar inda ya bayyana cewa masu ruwa da tsaki irin nasa sun yi watsi da “sababbin sojoji” a cikin jam’iyyar PDP.
A cewarsa rigingimun da ake fama da su a jam’iyyar na da nasaba da kokarin bata masa damar siyasa.

Lamido ya dage cewa matakin da ya dauka na shari’a ba wai don tilastawa kansa shugabancin jam’iyyar ba ne sai dai don kare abin da PDP ta gada da kuma kare masa hakkinsa da ya ce an tauye shi.
Ya kuma jaddada cewa kamar yadda al’amura ke tafiya Umar Damagum da Samuel Anyanwu na ci gaba da zama halastattun shugabannin jam’iyyar har sai wa’adinsu ya kare a ranar 8 ga Disamba 2025.
Ya kuma yi gargadin cewa barin jam’iyyar ta ci gaba ba tare da tsantsar tsarin shugabanci ba zai iya kawo cikas ga makomar masu son tsayawa takara da masu yi wa mukamai hidima da masu shirin sake neman mukamai.
“Ina matsawa a kafa kwamitin riko ina kira ga Wike Damagum da sauran su da su yafe wa juna su goyi bayan kafa kwamitin riko na bai daya,” in ji Lamido.
Ya bukaci shugabannin jam’iyyar PDP da su kira taron hadin gwiwa don magance kalubalen da jam’iyyar ke fuskanta tare da mayar da ita matsayin da ta dace a siyasar kasa.
Lamido ya kuma yi kira ga magoya bayansa da su kwantar da hankalin su su kuma yi hakuri har zuwa ranar 8 ga watan Disamba domin ganin yadda lamarin ke gudana.