Majalisar dattawan Najeriya ta amince da wani kudiri da ya ware satar mutane a matsayin wani nau’i na ta’addanci tare da yin kira da a yi gyara ga dokar ta’addanci domin ganin an zartar da hukunci mafi tsauri.
A zaman da aka yi a ranar Laraba Da ta gabata ‘yan majalisar sun amince cewa, duk mutumin da aka samu da laifin yin garkuwa da mutane tou ya fuskanci hukuncin kisa da zarar an yi wa dokar kwaskwarima.
“Kudirin ya ba da umarnin cewa, idan aka same shi da laifin yin garkuwa da mutane, dole ne a aiwatar da hukuncin kisa,” in ji Majalisar Dattawa.
‘Yan majalisar sun jaddada cewa, an dauki wannan matakin ne domin dakile matsalar tare da aikewa da kakkausar murya ga masu aikata laifuka.
Aisha. Yahaya, Lagos