Hambararren shugaban kasar Guinea-Bissau Umaro Sissoco Embalo ya isa Brazzaville babban birnin Jamhuriyar Congo, kwanaki bayan da sojoji suka kwace mulki, kamar yadda wata majiya ta kusa da shi ta bayyana.
Sojoji sun hambarar da gwamnatin Embalo a ranar Laraba da ta a gabata kafin a bayyana sakamakon zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki a karshen mako, wanda ke ci gaba da zaman dar-dar na siyasa a karamar jihar da ke magana da harshen Portugal.
Da farko Embalo ya bar Bissau zuwa makwabciyar kasar Senegal a wani jirgin sama na musamman, yayin da jami’an soji suka dora Manjo-Janar Horta Inta a matsayin shugaban rikon kwarya a ranar Alhamis da ta gabata
Majiyar wacce ta nemi a sakaya sunanta ta tabbatar da cewa Embalo yana Brazzaville ba tare da yin karin bayani ba.
Labaran Afirka/Aisha. Yahaya, Lagos