Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta ce Amurka da Rwanda sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar samar da dala miliyan 228 a fannin kiwon lafiya a kasar dake gabashin Afirka wannan shi ne yarjejeniya ta biyu a karkashin sabuwar hanyar gwamnatin Trump na samar da agajin kasashen waje.
Kasar Kenya ta zama kasa ta farko a cikin wannan makon da ta kulla yarjejeniya da Washington a karkashin ‘Dabarun Kiwon Lafiya na Duniya na Farko na Amurka’ wanda gwamnatin ta bayyana a watan Satumba tare da kokarin inganta dogaro da kai na kasashen da ke da niyya wajen tafiyar da sassan kiwon lafiyarsu.
Dala miliyan 228 ne gwamnatocin biyu za su bayar.
Yarjejeniyar Rwanda ta tsara “cikakkiyar hangen nesa don ceton rayuka da karfafa tsarin kiwon lafiyar Rwanda” in ji ma’aikatar harkokin wajen kasar a ranar Juma’a yayin da take taimakawa wajen sanya Amurka “mafi aminci”.
Yarjejeniyar bayar da tallafin kiwon lafiya na zuwa ne kwana guda bayan shugaban kasar Ruwanda Paul Kagame da takwaransa na Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango Felix Tshisekedi sun tabbatar da aniyarsu ta cimma yarjejeniyar da Amurka ta kulla domin kawo karshen rikici a gabashin Kongo.
Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta ce, karkashin yarjejeniyar lafiya Amurka za ta baiwa kasar Ruwanda dala miliyan 158 don yaki da cutar kanjamau da zazzabin cizon sauro da sauran cututtuka. Kuɗin zai kuma ƙarfafa sa ido kan cututtuka da mayar da martani.”
Haka kuma gwamnatin Rwanda na shirin kara zuba jarin kiwon lafiyarta na cikin gida da dala miliyan 70 tare da daukar nauyin kudi mai yawa yayin da ake rage tallafin Amurka a hankali tsawon shekaru,” in ji sashen.
Har ila yau, yarjejeniyar za ta gina kan wani shiri da ke ganin fara jigilar kayayyaki marasa matuki, Zipline, na daukar kayayyakin kiwon lafiya na ceton rai a inda ake bukata tare da hadin gwiwa da kasar Rwanda in ji Sashen.
“Yarjejeniyar ta jaddada burin Rwanda na gina tsarin kiwon lafiya mai dogaro da kai daidaitawa, da fasaha” in ji Oliver Nduhungirehe ministan harkokin wajen Rwanda bayan ya sanya hannu kan yarjejeniyar da jami’an Amurka a Washington.