Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaba Tinubu Ya Gana Da Gwamnonin APC Shida

29

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da gwamnoni shida da aka zaba a karkashin jam’iyyar APC a fadar gwamnati da ke Abuja.

Gwamnonin da suka gana da shugaban kasar a bayan gida sun hada da na Jigawa, Umar Namadi; Edo, Monday Okpebolo; Ekiti, Biodun Oyebanji; Kogi, Usman Ododo; Sokoto, Aliyu Sokoto; da Kebbi, Dr. Nasir Idris.

Har yanzu dai ba a bayyana cikakken bayanin taron ba har zuwa lokacin da aka buga labarin. Taron na sirri wanda ya dauki kimanin sa’o’i biyu ana gudanar da shi ne bisa la’akari da kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta a baya-bayan nan.

Da ‘yan jarida suka nemi jin ta bakinsu, Gwamnonin sun ki yin magana.

 

Aisha. Yahaya, Lagos

Comments are closed.