Mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ya kaddamar da Shirin Tallafin Ilimi na Gidauniyar Aliko Dangote, tare da kira ga masu ruwa da tsaki da su sake jajircewa wajen gina makomar da kowane yaro ɗan Najeriya zai iya zama mai dogaro da kansa.
Shirin, wanda aka yi hasashen zai lakume Naira tiriliyan 1 a cikin shekaru goma masu zuwa, zai tallafa wa ɗalibai a matakai daban – daban ta hanyar shirye-shirye daban-daban da aka tsara.
Da yake jawabi a ranar Alhamis a Legas, yayin ƙaddamar da shirin tallafin karatu na ilimi, Mataimakin Shugaban ƙasar ya yaba da ci gaban da Dangote ya samu, yana mai cewa ilimi nauyi ne da waɗanda suka san ikonsa na kawo sauyi ke ɗauka.
Shugaban Gidauniyar, Alhaji Aliko Dangote, ya ce shirin tallafawa ilimi na shekara-shekara na ₦ biliyan 100 na Gidauniyar zai ƙarfafa ɓangaren ilimi na Najeriya tare da faɗaɗa damar samun ingantaccen ilimi ga matasa a duk faɗin ƙasar, tare da tabbatar da cewa duk waɗanda za su amfana za a zaɓe su ta hanyar tsari mai gaskiya da adalci.
Abdulkarim Rabiu