Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaban Kasa Tinubu Ya Yabawa Gwamnan Borno Kan Tubar Ci Gaba

130

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yabawa gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, bisa yadda yake ci gaba da saka hannun jari a fannin ilimi, kiwon lafiya da sufuri, da kuma inganta rayuwar ‘yan asalin kasar a kullum.

Shugaban wanda ya kai ziyarar aiki a jihohi uku na jihohin Borno, Bauchi, da Legas, ya isa Maiduguri ne a ranar Asabar din da ta gabata, inda ya zarce da kaddamar da reshen filin jirgin Muhammadu Buhari na kasa da kasa, da wani sabon karin kayan aiki na VIP, motocin lantarki, motocin bas-bas na cikin gida, babura masu uku, da makarantun firamare, kananan sakandare, da sakandare model guda uku

“Ina kaddamar da wannan makarantar firamare, karamar sakandare da manyan makarantun gaba da sakandire don daukakar Allah, da ci gaba da karatun yaranmu,” in ji Shugaba Tinubu.

Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Mista Bayo Onanuga, ya fitar ta bayyana cewa, shugaban kasar ya kuma halarci daurin auren Sadeeq Sheriff, Dan tsohon gwamnan jihar, Sanata Ali Modu Sheriff, da kuma mai dakinsa, Hadiza Kam Salem.

Shugaba Tinubu ya tsaya a matsayin uban ango, kamar yadda al’adar Kanuri da al’adun aure suka tanada, yayin da Gwamna Zulum ya kasance uban amarya wajen karbar kudin amaryar gargajiya na tsabar zinari.

Shehun Borno, Alhaji (Dr.) Abubakar Ibn Umar Garbai Al-Amin El-Kanemi ne ya shirya daurin auren a babban masallacin Maiduguri.

Taron ya samu halartar gwamnonin jihohi bakwai: Dikko Umaru Radda na jihar Katsina; Agbu Kefas na jihar Taraba; Mai Mala Buni na jihar Yobe; Sheriff Oborevwori na jihar Delta; Muhammad Inuwa Yahaya na jihar Gombe; Ahmadu Umaru Fintiri na jihar Adamawa; da Prince Dapo Abiodun na jihar Ogun, da kuma Sanatoci da ministoci.

Shugaban ya tashi daga Maiduguri zuwa jihar Bauchi da karfe 3:25 na rana agogon kasar.

Comments are closed.