Shugaban kasar Namibiya, Netumbo Nandi-Ndaitwah ya nada Mista Ebson Uanguta a matsayin gwamnan bankin Namibiya, na tsawon shekaru biyar daga ranar 1 ga watan Janairun 2026.
Uanguta ya maye gurbin Johannes Gawaxab, wanda aka sanar da tafiyarsa a watan jiya.
Uanguta ya kasance daya daga cikin mataimakan gwamnonin bankin Namibia tun daga watan Janairun 2012.
Ofishin shugaban kasar Netumbo Nandi-Ndaitwah ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa nadin Uanguta a matsayin gwamna na tsawon shekaru biyar.
An nada Gawaxab a watan Yuni 2020 kuma ya jagoranci babban bankin ta hanyar cutar ta COVID-19.
A karkashin mulkinsa, Namibiya mai arzikin albarkatun kasa ta zama wurin da kamfanonin makamashin duniya ke gudanar da bincike. Tana da burin fitar da danyen mai na farko a shekarar 2030, wanda zai iya sauya tattalin arzikinta
Reuters/Aisha. Yahaya, Lagos