Take a fresh look at your lifestyle.

Birtaniya Ta Amince Da Mayar Da Bakin Haure Angola Da Namibiya

5

Angola da Namibiya sun amince da mayar da bakin haure da masu aikata laifuka ba bisa ka’ida ba, bayan da gwamnatin Burtaniya ta yi barazanar zartas da hukuncin biza ga kasashen da suka ki ba da hadin kai, in ji ma’aikatar harkokin cikin gida ta Burtaniya da yammacin jiya Asabar.

Ma’aikatar cikin gidan ta ce Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo an cire ta daga ayyukan biza mai sauri da kuma fifiko ga VIPs da masu yanke shawara bayan ta kasa cika ka’idojin Biritaniya don inganta hadin gwiwa

Sakatariyar harkokin cikin gida Shabana Mahmood ta ce Birtaniyya za ta iya kara daukar matakai zuwa ga dakatar da biza ga DRC, sai dai idan “hadin gwiwa ya inganta cikin sauri.

Sakataren harkokin cikin gida ya kara da cewa “Muna sa ran kasashe za su yi wasa da ka’ida.

Yarjejeniyar dai ita ce babban sauyi na farko a sauye-sauyen da aka sanar a watan da ya gabata na mayar da matsayin ‘yan gudun hijira na wucin gadi da kuma gaggauta korar wadanda suka isa Biritaniya ba bisa ka’ida ba.

Sakatariyar harkokin wajen Birtaniya Yvette Cooper ta ce Burtaniya ta kori mutane sama da 50,000 da ba su da ‘yancin ci gaba da zama a watan Yulin bara, wanda ya karu da kashi 23 cikin 100 a lokacin da ya gabata, sannan ta umarci jami’an diflomasiyya da su mayar da martani a matsayin babban fifiko.

 

Reuters/Aisha.Yahaya, Lagos

Comments are closed.