Take a fresh look at your lifestyle.

Wike Ya Yabawa ‘Yan Majalisar Ribas Saboda Goyon Bayan Shugaba Tinubu

25

Ministan babban birnin tarayya, Mista Nyesom Wike, ya yabawa ’yan majalisar dokokin jihar Ribas bisa tsayin daka da kare abin da ya dace a jihar tare da mara masa baya da kuma shugaban kasa Bola Tinubu.

Ministan ya yi wannan yabon ne a ranar Asabar din fa ta gabata a lokacin da ya ziyarci ‘yan majalisar a zauren majalisar da ke Fatakwal, babban birnin jihar.

Wike ya ce ‘yan majalisar sun nuna amana da iya jagoranci da tsayawa kan ka’idojin da suka dace.

Ya bukace su da su ci gaba da tsayawa kan abin da ya dace, yana mai cewa sun nuna kuma sun yi fice a kasar nan a matsayin ginshikin dimokuradiyya.

Ya yi Allah-wadai da matakin da ya sa Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara ya hana su hakkokinsu kafin ayyana dokar ta-baci.

Ministan ya ce; “Yana da muhimmanci mu zo wurin ‘yan majalisar dokokin jihar mu ce mun gode da abin da kuka yi mana da kuma al’ummar jihar Ribas, na ce kuma na gode da kyautar mota.

“Don haka a yau kun yi fice a kasar nan a matsayin ginshikin dimokuradiyya, ta yaya za a hana zababbun hakkinsu kawai saboda rashin jituwa da ku, iyalan ku sun tsaya kyam tare da ku.

“Ba zai zama rashin adalci a bangarenmu ba mu kai ga 2026 domin a shekarar 2025 duk wadanda suka tsaya tare da ku, da wadanda suka yi aiki tare da ku, ba ku ce musu na gode ba, kuma kuna bukatar ku gaya musu na gode, lokacin da na shigo nan, sai na ji zuciyata ta taba ni, duk wanda ya shiga wannan katafaren, na yi tunanin da yanzu wannan rukunin ya cika da ciyawa.

Wike ya kara da cewa “Ban san wata jihar da za ta ce zauren majalisar dokokin jihar su na da kyau kamar wannan. Me ya nuna, shugabanci.

 

Aisha. Yahaya, Lagos

 

Comments are closed.