Take a fresh look at your lifestyle.

A Daina Barin Lalatattun Motoci Akan Manyan Hanyoyi – Minista Yayi Gargadi

54

Ministan Ayyuka David Umahi ya yi gargadin cewa ba za’a daina yarda da fasa-kwaurin ababan hawa da busar da amfanin gona da aka noma a kan manyan titunan gwamnatin tarayya biyo bayan wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da wani dan damben nan Anthony Joshua a kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan. 

Umahi wanda ya jajanta wa Anthony Joshua da iyalan mutanen biyu da suka rasa rayukansu a hatsarin ya ce binciken farko ya nuna cewa ajiye motoci ba bisa ka’ida ba a kan titin ya taimaka wajen hadarin.

A cewar ministan wannan bala’in abu ne da ba za’a iya kauce masa ba ya kuma bayyana illolin da ke tattare da fakin ajiye motoci da sauran abubuwan da suka sabawa doka a manyan tituna.

Ya bayyana cewa ma’aikatar ayyuka ta kuduri aniyar aiwatar da umarnin da ta bayar a baya na hana ajiye motoci musamman manyan motoci a manyan titunan gwamnatin tarayya.

Umahi ya sanar da cewa daga watan Fabrairun 2026 za’a tura wata tawaga ta musamman da ta kunshi jami’ai daga ma’aikatar da kuma hukumomin tsaro da abin ya shafa domin tabbatar da bin umarnin.

“Ma’aikatar tana aiki tare da jami’an tsaro da kiyaye manyan tituna don tabbatar da cewa ba a bar motocin da suka lalace su ci gaba da zama a kan babbar hanyar ba, kuma babu wani mutum da aka yarda ya yi amfani da hanyoyin don bushewa da amfanin gonakinsu” in ji shi.

Ministan Ayyuka ya kuma bayyana aukuwar gobara da ta afku a kasuwar Balogun da ke Legas a kwanakin baya wadda ta yi sanadin salwantar rayuka da asarar dukiyoyi na miliyoyin Naira.

Ya nuna alhininsa game da faruwar lamarin tare da jajantawa iyalan wadanda suka rasa ‘yan uwansu da abin dogaro da kai.

Umahi ya bayyana fatansa na cewa, gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar Legas zasu hada kai domin dakile illolin da bala’in ya shafa.

 

Comments are closed.