Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaba Tinubu Ya Jajantawa Chimamanda Adichie akan Rasuwar Dan ta

53

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jajanta wa shahararriyar marubuciya Ms. Chimamanda Ngozi Adichie da iyalanta bisa rasuwar danta Nkanu Nnamdi inda ya bayyana rashin a matsayin daya daga cikin abubuwan da suka fi muni a rayuwa.

 

A cikin wata rubutacciyar sakon ta’aziyya da ya aikewa da kansa shugaban ya ce a matsayinsa na iyaye da su ma suka jure da radadin rashin wanda suke so ya fahimci cewa babu wani bakin ciki da ya kwatanta da bakin cikin rashin yaro.

 

Shugaba Tinubu ya ce tunaninsa da addu’o’insa suna tare da Ms. Adichie da mijinta Dokta Ivara Esege da daukacin ‘yan uwa a wannan mawuyacin lokaci inda ya bayyana cewa yana cikin bakin cikin su.

 

Shugaban Najeriyar ya bayyana Madam Adichie a matsayin jarumar adabi da ayyukanta suka sanya farin ciki da zaburarwa ga gidaje a fadin duniya sannan ya yi addu’ar Allah ya ba ta da iyalanta ikon jure rashin da ba za a iya kwatantawa ba.

 

Shugaban ya yi addu’ar Madam Adichie da ‘yan uwanta su samu karfin gwuiwa a cikin wannan mawuyacin lokaci ya kuma ba su tabbacin cewa tunaninsa da addu’o’insa na tare da su.

 

Chimamanda Ngozi Adichie shahararriyar marubuciyar Najeriya da mijinta Dokta Ivara Esege an jefa su cikin jimame a ranar 7 ga watan Janairu sakamakon rashin dansu dan biyu mai watanni 21 Nkanu Nnamdi Esege wanda ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya.

Comments are closed.