Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamnatin Tarayya Najeriya ta Kara Jaddada Kudurinta na Sake Farfado da Yankin Arewa Maso Gabashin Kasar.

TIJJANI USMAN BELLO.

0 374

Shugaba Buhari ya fadi haka ne a wajen taron kaddamar da Rukunin gidaje sama da Dari 8, wanda Hukumar kula da Bunkasa ci gaban Birane ta UNDP ta Majalisar Dinkin Duniya gami da hadin gwiwar gwamnatin jihar Borno, a Kauyen Ngarnam dake Yankin Karamar Hukumar Mafa a jihar Borno dake Arewa maso gabashin Najeriya.

 

Shugaba Buharin wanda Shugaban Ma’aikatan a fadar gwamnatin Kasar Farfesa Ibrahim Gambari, ya wakilta, ya bayyana cewar ” Babu shakka Yankin Arewa Maso Gabashi ya sha fama da ayyukan ta’addacin Boko Haram na wani lokaci abin da ya yi sanadiyyar lalacewar al’amura, irin su harkokin Ilimi, Kiwon Lafiya, Aikin Gona, Kasuwanci abin da kuma ya haifar da dai-daicewar Al’umma da nufin gudun hijira,hakan abin bakin cikine ainun.”

 

Ya kuma kara da cewar” Dolene gwamnati ta mike tsaye wajen farfado da Yankin ta yadda al’umma zasu ci gaba da gudanar da rayuwarsu na yau da kullum cikin farin ciki da annashuwa, a don haka gwamnati za tayi iya kokarita wajen farfado da Yankin ta wajen samar da ababen more rayuwa ga dimbin alumman da abin ya shafa na wannan Yanki ta yadda harkokin Rayuwarsu zai inganta.”

 

 

Ya ce” Zamu ci gaba da inganta harkar tsaro, a wannan Yankin dama wasu sassan Kasar da matsala tsaro ya addsba, kana zamu ci gaba da inganta harkar Noma da Kasuwanci kafin wa’adinnu ya kawo karshe.” 

 

Anasa Jawabin gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, ya yi bayanin irin nasarorin da ya cimmane tun daga lokacin da ya kuduri aniyar komawa da ‘Yan gudun hijiran ya zuwa garuruwansu na asali, in da ya ce ” Wajibine a matsayinmu na Shuganni muga cewar alummamu sun kasance cikin kwanciyar hankali da lumana a duk in da suka kasance, ya ce hakan ba zai samuba har sai sun koma garuruwansu na asali.”

 

Ya ce “To kuma komawarsu garuruwansu na asali shine zai iya kawo karshen ayyukan ta’addacin, tare da samun cikakken zaman lafiya, da bunkasuwar tattalin arzikin jihar dama Kasa baki daya, ya ce a don haka mun kuduri aniyar maido da daukacin ‘Yan gudun hijira a cikin kankanin lokaci, tare da karfafa masu karfin gwaiwan zama a garuruwansu bayan komawarsu.” inji shi.

 

Shiko wakilin Hukumar ta UNDP ta Majalisar Dinkin Duniya, a Najeriya Muhammad Yahaya, ya fadi irin kokarin da Hukumarsu ta keyine na hadin gwiwa tare da gwamnatin jihar Borno ne wajen mayar da ‘Yan gudun hijiran ya zuwa garuruwansu na asali, in da ya ce” Mun gina gidaje sama da Dari 5,  ga su wadannan’Yan gudun hijiran, a wannan Kauye na Ngarnam, ta Yankin Karamar Hukumar Mafa, kuma ko wani Magidanci ko Matan Aure, an basu Jarin Kudi akalla Naira Dubu 50 zuwa Dubu 100, tare da Dabbobin da zasu kiwata.” inji shi.

 

Taron ya sami halartan Jakadun Kasashen Turai, Jamus, Japan, Newtheland, da kuma na Majalisar Dinkin Duniya a nan Najeriya, an kuma mikawa Mutane ‘Yan gudun hijira da suka koma wannan Kauye ta Ngarnam, gidaje masu Dakuna biyu, da Kudade har Naira Dubu 100 ga Magidanta, a yayin da Matan Aure aka basu Dabbobi don yin Kiwo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *