Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaban Najeriya Ya Jajantawa Gwamnatin Jihar Benuwai

0 222

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da hare-haren da aka kai a jihar Benue.

A wata sanarwa da shugaban ya fitar, ya ce ba za a amince da kashe rayukan makiyaya da manoma ba.

 “Kada wanda ya isa ya afkawa kowa saboda salon rayuwarsa. Haka kuma kada wani ya rama wa wasu zaluncin da aka yi musu.

 “Dukkansu ya kamata a dora musu alhakin abin da suka aikata, kuma a yi adalci.

 “Hakazalika ba abin yarda ba ne ga rayukan wadanda kawai ke gudanar da ayyukansu na jami’an ‘yan sanda da jami’an gwamnati su ma su rasa rayukansu. Gwamnati za ta hukunta wadanda suka kashe wadannan rayuka,” inji shi.

 

Abubuwa Don Bincike

Shugaban ya yi alkawarin ba gwamnatinsa cikakken goyon baya wajen taimaka wa gwamnan jihar, Samuel Ortom, gwamnatin jiharsa, da al’ummar Binuwai da dukiyoyi domin gudanar da bincike kan abin da ya faru.

 

 “Lokacin da irin wannan bala’i ya faru, dole ne mu tuna da cewa dukkanmu ‘yan Najeriya ne.

 

“Siyasa kuma ta kan kawo cikas ga abin da ya dace ga al’ummarmu. Sau da yawa, yana raba mu. A matsayinmu na wadanda ‘yan kasarmu suka ba wa amanar shugabanci,” inji shi.

 

Ya kara da cewa ya zama wajibi kasar nan ta yi duk abin da za ta iya don ganin an dinke baraka da kuma haduwar jama’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *