Take a fresh look at your lifestyle.

Taron Duniya: Shugaba Buhari Ya Isa Birnin Seoul

0 254

Shugaban Najeriy Muhammadu Buhari ya isa birnin Seoul na kasar Koriya ta Kudu domin halartar babban taron duniya na Bio Summit, 2022.

 

Shugaban wanda ya sauka a filin tashi da saukar jiragen sama na Incheon da sanyin safiyar ranar Litinin ya samu tarba daga jakadan Najeriya a Koriya ta Kudu, Ali Magashi tare da wasu jami’an kasar Koriya.

 

Shugaban Najeriyar zai halarci taron koli na farko na duniya wanda gwamnatin Koriya ta Kudu da Hukumar Lafiya ta Duniya suka shirya tare.

 

Taron na kwanaki biyu, wanda zai gudana daga ranar 25 zuwa 26 ga Oktoba, yana da “Makomar Alurar rigakafi da Lafiyar Halittu” a matsayin takensa.

 

Najeriya na halartar taron ne tare da wasu kasashen Afrika biyar kuma ana sa ran shugaba Buhari zai gabatar da jawabin na Najeriya a wajen taron.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *