Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaba Buhari ya taya shugaban kasar Sin Jinping murna

0 395

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya shugaban kasar Sin Xi Jinping murnar lashe zabe mai dimbin tarihi a karo na uku a matsayin shugaban jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin.

 

A cikin wani sako, shugaban na Najeriya ya ce “Ina fatan sake zaben ku zai share fagen zurfafa da dorewar kawance da hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare da za su amfana da juna ga kasashenmu biyu.

 

“Na yi imanin cewa, ci gaban ababen more rayuwa, kamar layin dogo, madatsun ruwa da gina tituna, da samar da wutar lantarki, da mu’amalar kasuwanci za su samu gagarumin ci gaba.”

 

An sake zaben Xi Jinping a babban taron jam’iyyar karo na 20, wanda aka gudanar tsakanin ranakun 16 zuwa 22 ga Oktoba, 2022.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *