Sama da Mayakan Boko Haram Dubu 81, ne a Halin Yanzu Suka Mika Wuya ga Rundunar Soja
TIJJANI USMAN BELLO
Bubban Kwamandan Rundunar Sojin Najeriya ta Operation Hadin Kai dake Yankin Arewa Maso Gabashin Najeriya, Manjo Janar Christopher Gwabin Musa, ya fadi hakan a wani taron Manema labarai da ya kira a Hedkwatar Rundunar dake Barikin Sojoji ta Maimalari a garin Maiduguri bubban birnin jihar Borno dake Yankin Arewa Maso Gabashin Kasar, a karshen makon da ya gabata.
A Cikin wani Majigin Bidiyon da Kwamandan ruko mai kula da sashin bayanan Sirri ta Rundunar Kanal Obinna Azuikpo, ya nunawa manema labarai har na tsawon mintoci 20, mai dauke da Manyan Makamai gami da Mutanen da ‘Yan Bindigan sukayi garkuwa das
Bubban Kwamandan ta Operation Hadin Kai, Manjo Janar Christopher Musa, ya fada cewar, Rundunarsu ta sami nasarori da dama a cikin Makwanni shida kacal, in da ya kara da cewar ” Baya ga Mayakan Boko Haram sama da Dubu 81 da suka mika wuya ga Dakarunmu, ya zuwa yanzu mun sami nasarar Kubutar da ‘Yan Matan Makarantar Sakandare na Chibok har guda 2.
Ya ce “Mun kuma samu nasarar Kubutar da Mutane wadanda Mayakan suka yi garkuwa dasu har guda 99, wanda a cikinsu akwai Mata 52, mun kuma kame Mayakan Boko Haram din masu dauke da Makami da yawansu ya haura 107, duk a cikin watanni biyunnan a kuma farmakin da muke kaiwa dandazon mayakan Boko Haramun din a Sansanonin su dake Dazukan gami da Tsaunukan Tafkin Chadi da na Sanbisa.”
Bubban Kwamandan, har ila yau, ya ce ” A yanzu haka Sansanonin Killace Mayakan Boko Haram din da suka mika wuya guda 3 da ake dasu duk sun cike, to amma gwamnati ta samar mana da wani wuri a Kauyen Gongulan dake Yankin Karamar Hukumar Jere, kuma a yanzu haka muna kokarin killacewa tare da samar da kayayyakin amfanin yau da kullum da nufin ci gaba da killacesu a wurin.”
Ya ce, “Duk wadannan nasarorin da muka samu, basu samuba sai tare da samun cikakken hadin gwiwa a tsakanin Rundunoni da Hukumomin Jami’an Tsaro, irinsu DSS, Rundunar’Yan Sanda, da Jami’an Tsaron Farin Kaya ta Civil Depence, da Rundunonin Sojojin Ruwa da na Sama, gami kuma da sauran wadansu Mutanen da suke taimaka mana da bayannan Sirri.”
Ya ce, a don haka muke kira ga sauran Jama’a da su ci gaba da bamu cikakken hadin kai da goyon baya don ganin an sami nasarar cimma abin da muka sanya a gaba na kawo karshen wannan Yanki cikin kankanin lokaci, kowa ya huta, ga su Mayakan Boko Haramun kuma ina kira garesu da su yarda su mika wuya ga Dakarunmu tun kafin wuri ya kure masu.”
A karshen taron Manema labaran Kwamandan Soja ta Runduna ta 7, Manjo Janar Waidi Sha’aibu, ya baje kolin ‘Yan Matan ‘Yan Makarantar Sakandare na Chibok guda 2 da suka sami nasarar Kubutarwa ga manema labaran, in da ya ce “ A wani gumurzun da mukayi da Mayakan Boko Haram, mun samu nasarar Kubutar da wadannan’Yan Mata har guda 2, Rejoice Sarki ,Yagana Fagu, tare da Yaransu da suka haifa ‘Yan Biyu, kuma a yanzu haka mun mikasu ga Likitoci a Asibitin Koyarwa ta Jami’ar Maiduguri.”
Yagana Fagu, ta nuna farin cikinta da samun daman kubuta daga Mayakan, in da ta ce ” Mun sha bakar wahala da musgunawa gami da yi mana Auren dole ga su mayakan, gashi kuma sun rabamu da Iyayenmu, to amma yanzu Sojoji Sun kubutar damu mun kuma samu ‘Yancin kanmu, za kuma mu hadu da Iyayenmu, mu kuma ci gaba da karatunmu, a don haka muna masu godewa wadannan Sojojin da suka yi sanadiyyar kubutar damu Allah ya saka masu da Alkhairi.”
Leave a Reply