Bankin Duniya Ta Amince Zata ba wa Zambia Rancen Dalar Amurka Miliyan 270
Aliyu Bello Mohammed, Katsina
Bankin Duniya ya ce ya amince da rancen dalar Amurka miliyan 270 ga kasar Zambiya don taimaka mata murmurewa daga annobar cutar korona.
Har ila yau, lamunin na da nufin rage tasirin tattalin arzikin da yakin Ukraine ke fama da shi da kuma shawo kan matsalar basussuka.
A karshen shekarar 2020 Zambia ta zama kasa ta farko a Afirka tun bayan bullar cutar da ta gaza biyan bashin da take bin ta.
A cikin watan Agusta, asusun ba da lamuni na duniya IMF ya amince da rancen dalar Amurka biliyan 1.3 don taimakawa Zambia wata babbar masana’antar tagulla ta sake fasalin basussukan da take bin ta.
Shugaban bankin duniya David Malpass ya bukaci sauran masu ba da lamuni da su taimaka wajen rage basukan da ake bin kasar Zambia.
Leave a Reply