Shugaban Najeriy Muhammadu Buhari ya isa Owerri, babban birnin jihar Imo domin bukin bude taron shekara ta 2022 da ja da baya ga jami’an ‘yan sanda.
Shugaban Najeriyar wanda ya sauka a filin jirgin sama na Sam Mbakwe International Cargo Airport Owerri, ya samu tarba daga gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma da babban sufeton ‘yan sanda, Usman Alkali.
A wani bangare na tafiyar sa, Gwamna Uzodinma zai karbi bakuncin shugaban kasar liyafar cin abincin rana nan take bayan bude taron.
Shugaban zai dawo Abuja a yau.
Leave a Reply