Amurka ta ce ta yi Allah-wadai da sake barkewar yakin da kungiyar ‘yan tawayen M23 ta kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo ta yi a ranar 23 ga Maris.
A cewar rahoton, fadan ya janyo hasarar rayuka da dama da suka hada da mace-mace da jikkata a tsakanin fararen hula.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka Ned Price ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, Amurka ta yi kira da a gaggauta dakatar da yakin, sannan kungiyar M23 ta janye daga matsayinta, ta koma shiga tattaunawar Inter-Congo, wato Nairobi.
Leave a Reply