Take a fresh look at your lifestyle.

Hukumar Kidaya Ta Karbi Sakamakon Aikin Shata Gundumomi A Jihar Katsina

Kamilu Lawal, Katsina

0 278

Hukumar kidayar jama’a ta kasa ta gabatar wa ofishin hukumar kidaya na jihar Katsina da sakamakon aikin shata gundumomi da aka gudanar a fadin jihar

Wakilin shelkwatar hukumar zaben ta kasa Mr Izuwa Emmanuel ne ya hannanta kundin sakamakon ga darekta mai kula da ofishin hukumar kidayar na kasa a jihar Katsina Alhaji Ishaq Lawal a wajen taron masu ruwa da tsaki akan bayanan matsugunnai na aikin shata gundumomi wanda ya gudana a birnin Katsina.

Jim kadan bayan karbar kundin sakamakon daga wakilin shelkwatar, darektan ofishin hukumar a jihar Katsina ya hannanta sakamakon ga Kwamishinan hukumar na kasa mai kula da jihar Katsina Alhaji Bala Almustapha Banye domin mika ma shugabannin kananan hukumomin jihar 34.

Da yake jawabi a wajen taron, Alhaji Bala Banye ya bayyana cewa gabatar da sakamakon aikin shata gundumomin wani mahimmin bangare ne daga cikin shirye shiryen da hukumar kidayar ta kasa keyi domin gudanar da kidayar kasa a tarayyar najeriya

“gabatar da sakamakon na da nufin bada dama ga masu ruwa da tsaki su yi duba akan sa da nufin yin gyare gyaren da aka iya samu kafin mika shi ga shugaban kasa wanda zai bada damar maida shi zuwa wata doka wato gazette a turance da za’ayi amfani da ita wajen gudanar da kidayar jama’a ta kasa da za’a gudanar a tarayyar Najeriya cikin shekarar 2023 mai zuwa.” In ji Alhaji Banye

Kwamishinan hukumar zaben yace abinda ke kunshe a cikin kundin sakamakon, ya kunshi matsugunnan dake a cikin kowace gunduma da aka shata a fadin jihar.

kazalika yace an fitar da kundin kowace karamar hukuma daga cikin kundin jihar domin hannanta wa kowace karamar hukuma da nufin ba masu ruwa da tsakin damar duba shi daki- daki.

Tun farko, a nasa jawabin a wajen taron darektan ofishin hukumar kidayar na jihar Katsina Alhaji Ishaq Lawal ya bayyana cewa an shirya taron masu ruwa da tsakin ne domin karbar aikin matsugunnai na gundumomin da aka shata a lokacin aikin shata gundumomin da aka gudanar a fadin jihar.

Yana mai cewa bayan karbar sakamakon ana sa ran masu ruwa da tsaki a wajen taron za su tattauna akan sakamakon da nufin yin duba domin bada shawarwari ko yin gyara a idan bukatar hakan ta taso.

Taron masu ruwa da tsakin akan sakamakon aikin matsugunnan na aikin shata gundumomin ya samu halartar shugabannin kananan hukumomi da hakimai da dagattai da kuma jami’ai daga hukumomin NOA da INEC da kuma wakilin ma’aikatar kananan hukumomin jihar.

Dukkanin masu ruwa da tsakin sun jaddada kudurin su na bada gudummuwa domin samun nasarar aikin kidayar a shekarar 2023 mai zuwa.

Abubuwan da suka gudana a wajen taron sun hada da hannanta kundin sakamakon aikin shata gundumomin ga dukkanin shugabannin kananan hukumomin jihar 34.

Kazalika, masu ruwa da tsakin sun tattauna akan sakamakon da aka gabatar a gaban su dangane da abinda ke gaba akan gudanar da babban aikin kidayar jama’ar a shekarar 2023 mai zuwa.

 

Abdulkarim

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *