Shugaban Namibiya, Hage Geingob ya zargi kasashe masu arziki da rashin gaskiya a lokacin da suke magana kan yaki da sauyin yanayi.
Da yake magana da manema labarai a wajen wani taron da ake yi na COP27 a Masar, shugaba Geingob, ya ce kasashe masu arziki, wadanda ya dora alhakin rikicin da ake ciki, sun mayar da taron sauyin yanayi zuwa shaguna na tattaunawa.
Ya ci gaba da bayyana manyan masu gurbata muhalli a duniya a matsayin ‘masu aikata laifuka’ da kuma kasashe matalauta na duniya a matsayin ‘masu fama da su.
A halin da ake ciki, Shugaban Malawi, Lazarus Chakwera shi ma yana da sako mai zafi ga kasashe masu arziki.
Da yake jawabi a wurin taron, Mista Chakwera ya ce, ya kamata kasashe masu arziki su kara daukar nauyi wajen yaki da sauyin yanayi.
“Dukkanmu muna daidai da kima a gaban Allah, amma wajibcinmu, iyawarmu, damarmu, da laifukanmu sun bambanta.
“Saboda haka a matsayinmu na Malawi, mun yi imanin cewa, dole ne a bayyana bambancin da ke tattare da laifi da iya aiki tsakanin kasashen da suka ci gaba a matakin da suke dauka na rage sauyin yanayi, daidaitawa da kuma samar da kudade,” in ji shi.
Leave a Reply