Take a fresh look at your lifestyle.

Dakarun ‘Yan Tawaye sun Kashe Mutane Biyu a DR Congo

Aliyu Bello, Katsina

0 413

Wasu ‘yan kungiyar Allied Democratic Forces sun kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da wasu 10 a yankin Kabasha da ke kusa da birnin Beni a arewa maso gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango.

Wannan dai na zuwa ne biyo bayan farmakin sama da sojojin Kongo suka kai wa kungiyoyin ‘yan bindiga a garuruwan Runyoni, Musangati, Chanzu, da Bunagana da ke gabas mai fama da rikici.

A halin da ake ciki kuma akwai rahotannin da ke cewa an katse kauyuka da dama da ‘yan tawaye suka kwace a garin na Rutshuru, lamarin da ya sa mazauna yankin ba su da abinci da kuma agajin gaggawa.

Yayin da sama da mutane 90,000 suka rasa matsugunansu sakamakon sake barkewar fada a yankin a cikin ‘yan watannin da suka gabata, a cewar kungiyoyin agaji.

Gwamnatin DR Congo ta zargi makwabciyarta Rwanda da goyon bayan kungiyar M23 ta hanyar ba su tallafin kayan aiki da kudi. Rwanda ta sha musanta wadannan zarge-zarge.

Shugaban kasar, Félix Tshisekedi a makon da ya gabata ya bukaci matasan da su kafa kungiyoyin sa-kai da kuma shiga aikin soja don kare kasar daga hare-haren da kungiyoyin masu dauke da makamai ke kai wa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *