Take a fresh look at your lifestyle.

Ambaliyar Ruwa: Kasar Switzerland Ta Ba Da Gudunmawar Dala 756,000 Don Tallafawa Wadanda ambaliyar ruwa ya shafa

0 146

Gwamnatin kasar Switzerland ta bada tallafin sama da dalar Amurka dari bakwai ga gwamnatin Najeriya a matsayin agajin gaggawa ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa.

 

 

 

Matakin dai ya kasance martani ne ga roko na gaggawa da kungiyar agaji ta Red Cross da Red Crescent ta yi, na tallafa wa ayyukan jin kai na bala’in ambaliyar ruwa a Najeriya.

 

 

 

A cikin wata sanarwa da jakadan kasar Switzerland a Najeriya Nicolas Lang ya fitar, ya ce sama da mutane miliyan uku ne ambaliyar ruwa ta shafa a jahohi 34, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 600 tare da raba sama da mutane miliyan 1.5 da muhallansu.

 

 

 

“Ta hanyar wannan gudummawar, IFRC da kungiyar agaji ta Red Cross ta Najeriya za su hada kai da kokarin gwamnatin Najeriya na magance rikicin. Mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a jahohi 18 za a ba su taimakon bangarori daban-daban don biyan bukatunsu na yau da kullun.

 

Wannan zai hada da matsuguni na wucin gadi, sake gina gidaje, bayar da tallafin kudi iri-iri, da kuma matakan kiwon lafiya, da ruwa da kuma tsaftar muhalli don hana ci gaba da yaduwar cutar kwalara,” in ji ofishin jakadancin Switzerland.

 

 

 

Mista Lang ya bayyana jin dadinsa, inda ya ce kasar Switzerland na iya taimakawa Najeriya da al’ummarta domin shawo kan wannan matsala.

 

 

 

“Wannan gudummawar ga roko na gaggawar ambaliyar ruwa na IFRC ya yi daidai da tsayin daka da hadin gwiwar Switzerland da Najeriya, gami da bayar da agajin jin kai ga mutanen da rikicin ya shafa.

 

 

 

 “Tare da dimbin masu aikin sa kai a fadin kasar nan da kuma hadin gwiwa na kut da kut da hukumomin gwamnati da ke daidaita martanin, ina da yakinin cewa IFRC da kungiyar agaji ta Red Cross ta Najeriya za su samar da ingantacciyar amsa da jagoranci a cikin gida ga bukatun dubban ‘yan Najeriya. wadanda ambaliyar ruwa ta yi wa rayuwarsu illa,” in ji Ambasada Lang.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *