A lokacin da yake jawabi yayin bude wannan bubbar Kasuwar Kasa da
kasa ta Dabbobin a garin Gamboru a Yankin Karamar Hukumar Ngala, dake
da tazarar nisan kilo mita sama da 130, daga garin Maiduguri bubban
birnin jihar Borno, da kuma ya hade kan iyakansa da Jamhuriyar
Camaroun.
Gwamnan jihar Barno Babagana Umara Zulum , ya ja kunnen daukacin ‘Yan
kasuwar dabbobin da su guji tsunduma kansu a harka irin ta Boko
haram, ya ce’’ Duk wani Dan kasuwar Shanun da aka kama da hannu
dumu-dumu da wanda zai kai ga sake rufe kasuwar to ko zai dandanama
aya tsaki, a don haka ina horonku da ku guji aikata wasu munanan
dabi’u ku rike harkar kasuwancinku wanda zai iya kaimu ga habaka
tattalin arzin jihar dama Kasa baki daya.’’
Ya ce’’Bude wannan Kasuwa zai ci gaba da habaka tattalin arzikin
Kasa ganin cewar Kasuwace wacce ta hade Kasashen Camaroun zuwa Africa
ta Tsakiya, to kuma za muyi kokarin cewar an samar da kayayyaki don
habaka kiwo da noma ta yadda za’a iya fitar dasu Kasashen Makwabta.’’
Hakazalika ina rokonku da ku ci gaba da baiwa Jami’an tsaro cikakken
hadin kai da goyon baya ta yadda za’a sami nasarar fatattakar ayyukan
ta’addanci a kasa baki daya.
Tun da farko sai da Kwamandan Bataliya ta 3 ta Sojojin Najeriya
Laftanar Kanar Tolu Adedokun, ya tabbatar da samun cikakken tsaro a
yankun to amma sai ya ce’’ Duk Dan kasuwar Shanun da aka kamashi da
hannu dumu-dumu yana hada kai da ‘Yan ta’addan Boko haram to za’a
hukuntashi kamar yadda doka ta tanadar, to kuma a ta bangaremu zamu ci
gaba da iya kokarinmu wajen samar da cikakken zaman lafiya a wannan
Yanki saboda haka muna rokonku da ku ci gaba da bamu cikakken hadin
kai da goyon baya don samun nasarar kawar da ayyukan ta’addanci.’’
A jawabin godiya a madadin ‘Yan kasuwar, Shugaban ‘Yan
Kasuwar Shanun Alhaji Yakubu, ya ce’’Zamu yi iya kokarinmu wajen bin
doka da oda don tabbatar da samun zaman lafiya a wannan kasuwan da aka
bude yau, kuma har ila yau zamu ci gaba da baiwa Jami’an tsaro
cikakken hadin kai da goyon baya don magance ayyukan ta’addanci a
wannan kasuwa, domin kuwa kowa ya dandana kudanrsa kuma abin ya shafi
kowa a don haka zamu hada hannu da jami’an tsaro don samun ingantuwar
kasuwancin dabbobi a wannan yankin.’’.
A karshe gwamna Zulum, ya rarraba kayayyakin Abinci da Tufafi har na
Miliyoyin Nairori ga ‘Yan gudun hijiran da suka koma wannan garin na
Gamboru Ngala da wasu garuruwan da suka yi gudun hijiran.
Leave a Reply