Gwamatin jihar Katsina ta gabatar da kasafin kudin shekarar 2023 na sama da Naira Biliyan Dari Biyu da Tamanin
Kamilu Lawal
Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ne ya gabatar da kasafin a wani zama na musamman a majalisar dokokin jihar dake birnin Katsina.
Aminu Masari ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta tsara kashe jimillar Naira Biliyan Dari Biyu da Tamanin da takwas da Miliyan Dari Shidda da Ashirin da Ukku da Naira Dubu Dari da Hamsin da Bakwai da Naira Dari Tara da Sittin da Ukku(288,623,259,963 00.) a kasafin kudin na shekarar 2023 mai zuwa
Yayi nuni da cewa a cikin kasafin an ware sama da Naira Biliyan Dari da Arba’in a matsayin kudin da za’a kashe wajen gudanar da manyan aiyuka yayin da akai kasafin sama da Naira Biliyan Dari da Hudu a matsayin kudin aiyukan Yau da Kullum
Da yake bayyana kaso da mahimman bangarori da ma’aikatun jihar suka samu a kiyasin kasafin, gwamna Masari yace ma’aikatar Muhalli Ita ta samu kaso mafi tsoka yayin da ma’aikatar Albarkatun Ruwa ke bi Mata a matsatin ta biyu sai ma’ikatar lafiya take zaman ta Ukku inda ma’aikatar Ilmi ke biye a matsayin ta Hudu daga cikin bangarorin da aka ware ma kaso mafi tsoka a kasafin kudin na 2023 mai zuwa
Ya bayyana cewa ana sa ran samun kudaden ne daga kudin shiga na cikin gida da aka kiyasta za’a samu da kuma kason da gwamnatin tarayya zata baiwa jihar a tsawon shekarar ta 2023 mai kamawa.
Leave a Reply