Take a fresh look at your lifestyle.

Dan Bindiga Ya Kashe Mutane 10 A Wani Hari Da Aka Yi A Walmart A Virginia

Theresa Peter

0 166

Akalla mutane 10 ne suka mutu lokacin da wani dan bindiga ya bude wuta a wani babban kanti na Walmart da ke Chesapeake a jihar Virginia ta Amurka a daren ranar Talata.

 

 

 

Leo Kosinski, mai magana da yawun hukumar ‘yan sandan Chesapeake, ya fada a wani takaitaccen taron manema labarai cewa an tsinci gawar dan bindigar a shagon.

 

 

 

Kosinski ya ce ana kyautata zaton harbin ya faru ne a cikin shagon, kuma wanda ake zargin ya aikata shi kadai.

 

 

 

Akwai ‘yan cikakkun bayanai, amma wani jami’in ‘yan sanda ya yi magana game da mutuwar mutane fiye da 10 da kuma jikkata da dama. Babu wani dalili da ya fito.

 

 

 

‘Yan sanda sun shaida wa manema labarai cewa harin ya faru ne da karfe 22:12 agogon kasar (03:12 agogon GMT).

 

 

 

Walmart ya fada a cikin wata sanarwa da sanyin safiyar Laraba cewa “mun yi matukar kaduwa a wannan mummunan lamari a shagon mu na Chesapeake, Virginia.”

 

 

 

“Muna yin addu’a ga wadanda abin ya shafa, al’umma da abokanmu.

“Muna aiki tare da jami’an tsaro, kuma muna mai da hankali kan tallafawa abokanmu.”

 

 

 

Karanta kuma: An kashe mutane biyar, 18 sun jikkata a harbin wani gidan rawa na Colorado

 

 

 

Sanatan jihar Virginia, L. Louise Lucas, kuma ‘yar jam’iyyar Democrat, ta kara da cewa “ta yi matukar baci”.

 

 

 

Ta rubuta a shafinta na Twitter cewa: “Ba zan huta ba har sai mun nemo hanyoyin kawo karshen wannan annoba ta bindiga a kasarmu.”

 

 

 

 

Harin na yammacin Talata na zuwa ne kwanaki kadan bayan da wani dan bindiga ya bude wuta a wani gidan rawa na LGBT a jihar Colorado ta Amurka, inda ya kashe mutane biyar tare da jikkata wasu 17.

A cikin 2019, wani harbin jama’a a Walmart a garin El Paso a Texas ya yi sanadin mutuwar mutane 23.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *