SDP: Dan Takarar Shugaban Kasa zai aderishin Magance Kalubalen Tattalin Arziki, Rashin Tsaro, Talauci
Aliyu Bello Mohammed, Katsina
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), Prince Adewole Adebayo, ya ce zai magance talauci, rashin tsaro da magance duk matsalolin tattalin arzikin da ke damun kasar, idan aka zabe shi a matsayin shugaban Najeriya a 2023.
Ya yi kira ga ’yan Najeriya da su zabi shugabannin da za su bauta wa Allah da kuma bil’adama.
Prince Adebayo ya yi wannan kiran ne a wani taron tattaunawa da kungiyar kiristoci ta Najeriya (CAN) ta shirya a Abuja ga daukacin ‘yan takarar shugaban kasa gabanin zaben shugaban kasa na 2023.
Leave a Reply